GONI: MAJALLAR ILIMIN ALKUR’ANI

Cibiyar Nazari akan Alkur’ani da ke Jami’ar Bayero ta Kano, ta kudurta wallafa Majalla da harshen Hausa wadda musamman za ta dukufa wajen hidima ga ilimin Alkur’ani. Majallar za ta gabatar da bincike da bayanai da labarai da suka shafi fannonin ilimin Alkur’ani. Manufar Majallar ita ce samar da wani dandali da malaman Alkur’ani za su baje kolin ilimin Alkur’ani domin kusantar da fahimtarsa ga al’umma.
Majallar za ta zakulo ababen alfaharinmu na tarihin ilimin Alkur’ani a wannan kasa, musamman fannonin iliminsa da malaman wannan kasa suka yi fice a kai. Don haka za ta fuskantar da bayanai akan kafuwar makarantun tsangaya da yaduwar ilimin Alkur’ani da tarihin fitattun Alaranmomi da Gwanaye na da da na yanzu da yanayin tsare-tsarensu wajen habaka koyon karatun Alkur’ani. Majallar za ta kuma yi kokarin fayyace bayanai na malamai da masana akan hanyoyin da suka dace a bi domin habaka makarantun Alkur’ani da tsangayu da inganta manhajarsu domin dacewa da muhimman bukatun al’ummar musulmi a yau.
Majallar Al-Goni za ta kunshi bayanai da labarai na ayyukan Cibiyar Bincike akan Alkur’ani da sauran cibiyoyi da makarantun Alkur’ani.

Dan karin bayani, danna nan Bukatar makaloli